IS ta kai sababbin hare-hare a Siriya
May 23, 2016Talla
Masu fafutuka da kuma masu sanya idanu kan yakin na Siriya sun tabbatar da afkuwar harin, inda shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya wadda ke da matsuguni a birnin London na kasar Birtaniya Rami Abdel Rahman ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa sama da mutane 48 ne suka hallaka a yankin Tartus yayin da wasu 73 suka rasa rayukansu a Jableh duk kansu da ke wajen gundumar Latakia. Hare-haren dai an kai su ne a tashoshin ababen hawa daban-daban da ke wadannan birane da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki da kuma mashigar sashen bada agajin gaggawa na babban asibiti da ke birnin Jableh. Tuni dai kungiyar 'yan ta'addan IS ta bayyana cewa ita ce ke da alhakin harin.