Mutane da dama sun mutu a samamen Idlib
December 17, 2019Akalla fararen hula 14 sun rasa rayukansu yayin da 18 suka ji munanan raunuka a lokacin da dakarun gwamntin Siriya suka harba bama-bamai a lardin Idlib da nufin maida yakin karkashin ikonsu. kanfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa wasu daga cikin bama-baman sun fada a tsakiyar kasuwar kauyen Maasran, inda fararen hula suka mutu yayin da shaguna da gidaje da dama suka lalace.
Gamayyar kungiyoyin da ke kare hakkin bil Adama ta kasar ta nunar da cewa fada ya sake rintsabewa tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye a yankin Arewa maso yammacin Siriya duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin biyu suka cimma a watan Agustan da ya gabata.
Tun a watan Oktoba ne shugaba Bashar al-Assad ya kai ziyara yankin Idlib inda ya ce karbe lardin daga hannun 'yan tawaye ne kawai zai iya kawo karshen yakin da aka shafe shekaru takwas ana fama da shi a Siriya. Mutane dubu 370 ne suka rigamu gidan gaskiya yayin da miliyoyi suka kaurace wa matsugunansu tun bayan barkewar yakin Siriya a shekara ta 2011.