1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake ya girgiza wani masallaci a Kabul

November 21, 2016

Harin da aka kai kan 'yan Shi'a masu bikin Arba'in na Imam Hussein a wani masallaci da ke birnin Kabul ya hallaka mutane akalla 27.

https://p.dw.com/p/2T0mq
Afghanistan Anschlag auf Moschee in Kabul
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Akalla mutane 27 suka rasu sannan wasu 35 sun samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wani masallacin 'yan Shi'a na Baqir-al-Olum da ke yammacin Kabul babban birnin kasar Afghanistan. Kamar yadda 'yan sanda suka nunar an tada bam din ne lokacin bikin Arba'in na Imam Hussein da 'yan Shi'a ke gudanarwa a wannan Litinin, da ya zo daidai da kwanaki 40 bayan bikin Ashura. Wani mai suna Sayed Ali da ya shaida lamarin da idonsa cewa yayi.

"Ni da kaina na taimaka wa dakarun tsaron Afghanistan wajen daukar gawarwaki 30 zuwa 35 daga cikin masallacin, sannan fiye da mutane 100 sun jikkata sakamakon fashewar bam din."

A Afghanistan dai 'yan Sunni masu tsattsauran ra'ayi na yawaita kai hari kan 'yan Shi'a a lokutan bukuwan irin wannan. Sai dai kungiyar Taliban ta musanta hannunta a harin, inda kakakinta Zabihullah Mujahid ya ce ba su taba kai hari kan masallaci ba, domin ya saba wa manufarsu.