1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da yawa sun rasu a wani harin bam a shelkwatar 'yan sanda a Masar

December 24, 2013

Hukumomin kasar sun kuduri aniyar zakulo wadanda ke da hannu a harin don gurfanar da su gaban kuliya.

https://p.dw.com/p/1AgWT
Hoto: Reuters

Alkalumman hukumar kasar Masar sun ce akalla mutane 12 suka rasu sannan wasu 134 suka jikata a wani harin bam da aka kai kan shelkwatar 'yan sanda da ke birnin Mansura da ke arewacin kasar. Daga cikin wadanda suka rasu kamar yadda ma'aikatar cikin gida da kuma ta kiwon lafiya suka nunar akwai 'yan sanda 10 da farar hula biyu. A wata ziyara da ya kai garin Nile-Delta mai nisan kilomita 120 arewa da birnin Alkahira, ministan cikin gida Mohammed Ibrahim ya yi alkwarin zakulo abin da ya kira 'yan ta'adda da suka aikata wannan ta'asa.

"Dukkanmu daga kai na har izuwa soja mafi karancin mukami, mun sha alwashin karya lagon wadannan 'yan ta'adda. Wannan aika-aika ba za ta taba ba mu tsoro ba, sai ma akasin haka, za ta karfafa mana guiwa a yakin da muke don tarwatsa 'yan ta'adda."

Wannan harin dai shi ne irinsa na farko mafi muni tun bayan hambarar da gwamnatin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a cikin watan Yuli da ya gabata.

Mawallafa: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman