Yakin Sudan da Kwango sun kara adadin yawan masu hijira
May 14, 2024Talla
Yakin basasar Sudan da na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na daga cikin muhimman rikice-rikicen da suka kara adadin 'yan gudun hijira na cikin gida mafi muni a duniya a baya-bayan nan, in ji kungiyar da ke sa ido kan masu hijira sakamakon rikice-rikice mai suna IDMC.
Kungiyar ta ce ko baya ga tagwayen yake-yaken basasar na Afirka, yakin da Isra'ila ke gwabzawa a zirin Gaza na guda daga cikin bala'o'in da suka kara yawaita adadin masu neman tsira da rai da ya kai har kaso 50 cikin 100.
Kazalika kungiyar ta ce kasar Sudan, ta kasance kasar farko da aka fi yawaitar 'yan gudun hijira na cikin gida a duniya, bayan mutane fiye da miliyan tara sun gudu don tsere wa yaki a cewar wani rahoto da kungiyar ta fitar.