1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sama da 70 sun mutu a harin Taliban

Gazali Abdou Tasawa
October 17, 2017

A Afganistan mutane 71 sun mutu a yayin da wasu 170 suka jikkata a cikin wasu tagwayen hare-hare da mayakan kungiyar Taliban suka kaddamar wannan Talata a wasu birane biyu na kasar na kan iyaka da Pakistan. 

https://p.dw.com/p/2m2MF
Afghanistan | beschädigte deutsche Botschaft in Kabul
Hoto: Reuters/M. Ismail

Mataimakin ministan cikin gida na kasar Janar Murad  Ali Murad ya ce  mutane 41 da suka hada da fararan hula 20 suka mutu a yayin da wasu 160 da suka hada da fararan hula 110 suka jikkataa harin da aka kai a wani ofishin 'yan sanda na garin Gardez na jihar paktiya ta Kudu maso Gabashin kasar. 

Harin na biyu a kai shi ne kusan a lokaci daya a birnin Andar na jihar Ghazni inda jami'an tsaro 25 da fararan hula biyar suka halaka. Wani kakakin Kungiyar Taliban ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kungiyarsu ce ke da alhakin kai wannan hari, wanda ya ce sun kai shi ne a matsayin martani ga jerin hare-haren da Amirka ta kaddamar a baya bayan nan da jirage maras matuka na Dron.