Mutane tara sun mutu a harin birnin Munich
July 23, 2016Matshin mai shekaru 18 da haihuwa, ya hallaka mutane guda tara tare da jikkata wasu 16 cikinsu har da yara kanana da dama, kafin daga bisani a samu gawarsa bayan da ya bindige kanshi. A cewar shugaban 'yan sandan birnin na Munich Hubertus Andrae, shi dai wannan matashi mutun ne da ba a san shi ba a ofishin 'yan sanda wajen aikata wasu laifuka:
" Tashin hankali ya soma ne tun da misalin karfe biyar da minti 50 inda muka samu labarin cewar ana harbe-harbe a cibiyar kasuwanci ta Olympic da ke yammacin birnin Munich. Kuma da farko dangane da bayanai da muka samu na shaidu, an ce mutanen uku ne suka kai harin kuma biyu sun bar wurin cikin wata mota a guje, amma kuma da ga baya mun gano cewar wannan mutun shi kadai ne ya kai wannan hari."
Tuni dai kasashen duniya suka yi ta jajentawa hukumomin na Jamus kan wannan hari, kuma a cewar shugaban Diflomasiyyar kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier, babu wani haske kan dalillan da suka sa wannan matashi yin hakan. Sai dai kuma sannu a hankali al'ammura sun fara daidaita a birnin na Munich bayan da a lokacin da harin ya faru aka soke duk wani tsani na suhuri a birnin tare da zuba jami'an tsaro a babbar tashar jiragen kasa da wasu mahimman wurare na birnin.