Mutum 14 sun mutu a harin Siriya
April 9, 2018Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban Amirka Donald Trump a ranar Lahadin da ta gabata, ya yi gargadin daukar mataki kan gwamnatin Bashar al-Assad bisa zarginta da amfani da makami mai guba akan al'umma a garin Douma, sai dai tuni fadar White House ta nesanta kanta daga kai wani hari kamar yadda ta fadi a wata sanarwar da ta fitar bayan aukuwar lamarin na yau.
Shekaru fiye da shida kenan da rikici ya barke a Siriya, dubban mutane sun rasa rayukansu an kuma zargi gwamnatin Assad da laifin amfani da makami mai guba a rikicin. Faransa da Amirka na daga cikin kasashen duniya da ke neman ganin an hukunta masu alhakin amfani da sinadarin Klorin mai matukar illa da aka ce an yi amfani da su akan jama'a a biranen Ghouta da kuma Douma inda aka samu asarar rayukan fararren hula.