1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum miliyan 11 na neman dauki a tafkin Chadi

August 30, 2018

Akalla mutum miliyan 11 ne ke bukatar jin kai na gaggawa a yankin nan na tafkin Chadi, da ke fama da matsalar tsaro.

https://p.dw.com/p/3442Y
Nigeria Boko Haram Anschlag Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP

Kungiyoyin agaji na duniya, sun ce akwai akalla mutum miliyan 11 ne ke bukatar jin kai na gaggawa a yankin nan na tafkin Chadi, da ke fama da matsalar tsaro da kungiyar Boko Haram ta sababta.

Kungiyoyin sun bayyana bukatar ne gabanin wani taron samar da kudadena tallafi da za a yi cikin makon gobe a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus.

Kasashen da lamarin ya fi tsanani a cikinsu dai sun hada ne da Chadin da Najeriya da Nijar da kuma Kamaru.

Kimanin mutum miliyan biyu da dubu 500 suka rasa sukuni, yayin da wasu miliyan biyar ke fama da karancin abinci, sanadiyar rikicin na Boko Haram.