Adadin wadnda suka mutu a harin tashar jirgin kasa sun karu
April 8, 2022A wata sanarwa da gwamnan yankin Donbass ya fitar jim kadan baya harin yace mutane 38 ne suka mutu kai tsaye a yayin da wasu 12 suka ce ga garinku bayan an garzaya da su a asibiti. Kana gwamnan ya kuma kara da cewa yanzu haka da akwai akalla mutun 98 da harin na rokar ya raunata.
Tuni kasashen yamma suka fara mayar da martani game da harin, shugaban kungiyar EU Ursula von der Leyen da yanzu haka ke ziyara a Ukraine ta kira harin da na rashin imani, a yayin da Amirka da Jamus da Faransa suka yi wa Rasha kakkausar suka. Birtaniya ta ambaci wani shiri na taimakawa Ukraine da makaman kakkabe roka don kare kanta, jim kadan bayan ta bi sahun Amirka inda ta kakaba takunkumi ga 'ya 'yan shugaban Rasha Vladimir Poutine da tsohuwar matarsa, hakan da kuma 'ya 'yan ministan harkokin wajen kasar Sergueï Lavrov.