1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Al-Baghdadi jagoran IS

June 16, 2017

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta ce tana gudanar da bincike don sanin ko harin sama da ta kai a kasar Syria ya halaka shugaban na IS Abu Bakr al-Baghdadi.

https://p.dw.com/p/2ep2F
Abu Bakr al-Baghdadi Bildnis in Flammen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Swarup

A yayin da ake ta kila wakala akan mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi, shugaban kungiyar IS mai da’awar jihadi, ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce tana gudanar da binciken sanin ko harin sama da ta kai a kasar Syria a baya ya halaka shugaban na IS. Rashar dai ta kai hari kan wani taron shugabanin kungiyar ta IS da ake kuma kyautata zaton Al-Baghadadin ya halarta a watan Mayun da ya gabata.

Kawo i yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomin Rasha suka fitar a hukumance na tabbatacin mutuwar shugaban na IS. Sai dai wata kafar labaran kasar ta SPUTNIK ta rawaito cewa bayanai daga ma'aikatar tsaron kasar ta yi bayanin cewa da yiwuwar hare- haren da ta kai akan taron mayakan kungiyar IS a birnin Raqqa a ranar 28 ga watan jiya,  ya yi sanadiyar mutuwar jagoran na IS da ma wasu kusoshin kungiyar. Akwai kuma wasu mayakan IS din kimanin 300 da suka rasa rayukansu a farmakin.

Ibrahim Abu Bakr Al-Baghdadi dai,  na daga cikin mutanen da Amirka ke nema ruwa a jallo bisa zargin kitsa hare-haren ta'addanci a sassa daban-daban na duniya.