1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Paproma Benedict na 16 ta girgiza duniya

Christoph Strack Lateefa Mustapha/Mouhamadou Awal
December 31, 2022

Shugabannin duniya na nuna alhinin mutuwar tsohon Paparoma Benedikt na 16 da ya jagoranci darikar Katolika. Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da shugaban Rasha Vladimir Putin sun nuna jimamin rashi da aka yi

https://p.dw.com/p/4Lb49
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

 Benedict na 16 ya kasance Paparoma na farko daga Jamus bayan kusan shekaru 500. A yayin da yake shugabancin mabiya darikar Katolika na duniya, ya kawo sauyi a ofishinsa, ya kuma yi fice wajen samun sabanin ra'ayi sau da dama da sauran shugabannin cocin. A yanzu ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 95 a duniya.

Zabar Benedict a matsayin paparoma a shekara ta 2005, ya janyo tsallen murna da alfahari daga Kiristoci mabiya darikar Katolika a Jamus. "Mun zama Fafaroma." Wannan shi ne abin da ya kasance kanun labarai a manyan mujallu. Sai dai duk da haka sun nuna damuwa, paparoman da ya kasance na 265 a tarihin Cocin na da shekaru 78 a wancan lokaci, abin da ake ganin zai kawo tarnaki wajen samun sauyi ga akidarsa ta ra'ayin 'yan mazan jiya. Shekaru 60 bayan yakin duniya na biyu da kuma kisan da masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa suka yi wa Yahudawa an samu paparoma daga Jamus daga kasar Martin Luther.

Joseph Kardinal Ratzinger
Paparoma Benedikt na 16 ke nan lokacin da aka nada shi a fadar vatikanHoto: Domenico Stinellis/AP Photo/picture alliance

"Manyan kadinal-kadinal sun zabe ni. Mutum mai saukin kai da tawali'u da ke kaskantar da kansa a fadar ubangiji."

Da wadannan kalamai, Kardinal Joseph Ratzinger ya shiga cikin Cocin St. Peter's Basilica da ke birnin Rum, kuma take ya samu karbuwa. Bayan kwanaki biyu kacal na zabe, farin hayaki ya fito daga ssaman cocin, abin da ke nuni da cewa mai shekaru 78 a wancan lokaci, ya zama fafaroma. 

An haifi Joseph Ratzinger a ranar 16 ga watan Afrilun 1927 a yankin Bavaria da ke Jamus. Babansa ya kasance dan sanda. Yana da shekaru 17 a duniya aka sanya shi cikin dakarun Wehrmacht na 'yan Nazi a karshen shekara ta 1944. A karshen shekarun 1950, Ratzinger ya zamo farfesan addini da nan da nan ya samu daukaka. Archbishop Joseph Fringsya bayyana cewa zai kasance guda daga cikin manyan limaman Kiristoci mabiya darikar Katolika daga shekara ta 1963, yayin babban taronsu da aka gudanar.

A shekara ta 1977 Ratzinger ya zamo Archbishop a Munich kuma ba da jimawa ba ya zamo Kadinal. Shekaru hudu bayan nan paparoma Johannes Paul II ya gayyato shi zuwa birnin Rum, inda aka ba shi matsayin babban jagoran addini. Sai dai dangane da batun kawo sauyi kan rawar da mata ka iya takawa da kuma tattalin arziki, Ratzinger ya kasance mai tsattsauran ra'ayin 'yan mazan jiya.