Mutuwar mutane kusan 100 ta janyo dokar ta baci a Bangladesh
July 20, 2024Tashin hankalin da ya barke a Bangladesh, ya tilastawa firaministar kasar Sheikh Hasina soke tafiye-tafiyen da ta tsara yi zuwa kasashen Spain da Brazil a ranar Lahadi, kamar yadda sakataren yada labaranta Nayeemul Islam Khan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.
Karin bayani:Ana ci gaba da zanga-zanga a Bangladesh
Tuni dai aka baza sojoji a biranen kasar yau Asabar, bayan arangamar da aka samu tsakanin dalibai da 'yan sanda da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 100. Sannan kuma an sanya dokar hana fita har zuwa ranar Lahadi.
Karin bayani:Bangladesh: An rantsar da Hasina a wa'adi na hudu a jere
Musabbabin zanga-zangar ya samo asali ne da wani tsarin daukar aiki da firaministar kasar ta bijiro da shi, da ya fifita iyalan mutanen da suka yi gwagwarmayar yakin neman 'yancin kan kasar daga Pakistan a shekarar 1971.
Wata sanarwa da kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Amnesty International ta fitar, ta nuna kaduwa da asarar rayuka da ake ci gaba da samu a dalilin tarzomar.