1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Sojan Indiya a Kwango

July 7, 2012

Ɗaya daga cikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Jamhoriyar Demokraɗiyyar Kwango ya rasu sakamakon harin da 'yan tawaye suka kai musu bayan sun yi musu wata ƙofar rago

https://p.dw.com/p/15TIS
Soldaten aus Paraquay der UN-Schutztruppe Monuc patroullieren durch Kinshasa im Kongo (Archivfoto vom 14.07.2006). Foto: Maurizio Gambarini dpa +++(c) dpa - Report+++
Dakarun wanzar da zaman lafiyaHoto: picture-alliance/dpa

Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya, ya yi Allah wadai da wani kwanton ɓaunan da wasu 'yan tawye suka yi wa wani rukunin dakarun wanzar da zaman lafiyar majalisar, a Jamhoriyar Demokraɗiyyar Kwango, wanda har ya yi sanadiyyar mutuwar wani soja, ɗan asalin Indiya.

Sojan ya gamu da ajalinsa ne sakamakon fashewar wani bam a daidai lokacin da 'yan tawayen da ake zargi suna samun goyon bayan Ruwanda, suka kutsa zuwa gabashin ƙasar.

Kwamitin ƙolin, mai mambobi 15 a ƙarƙashin jagorancin babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-Moon, ya fitar da sanarwar da ke kira ga 'yan tawayen, da a yanzu haka ake kyautata zaton sun fake a yankin gabashin Kwangon da su tsagaita wuta su kuma daina tashe-tashen hankula.

Kwamitin Sulhun ya nuna takaicinsa ƙwarai ga wannan ta'asa ya kuma buƙaci gwamnatin Jamhoriyar Demokradiyyar Kwangon da ta hukunta duk wanda aka kama da hannu wajen aikata wannan aika-aikar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar