Muzambik na neman agajin duniya
April 30, 2019Talla
A wata hirar da ya yi da tashar DW, firaministan ya ce bangaren abinci babu wata gagarumar matsala a yanzu, kayayyakin sake gina kasar ne babban kalubalen da ke a gabansu.
Kasar dai na fama ne da barnar da mahaukaciyar guguwa dauke da ruwan sama, da ta afka wa arewacinta a makon jiya.
Ofishin kula da agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya ce guguwar mai karfin gaske ce ta aka taba gani a yankin kudancin Afirka.
Majalisar ta duniya ta kuma yi hasashen ci gaba da shatata ruwan na sama cikin kwanakin da ke tafe.
Akalla mutum 38 suka mutu a sabon ibtila'in, wasu sama da dubu 23 kuwa suka rasa muhalli.