1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: 'Yancin masu neman jinsi

March 3, 2021

Ghana kamar sauran kasashe a nahiyar Afirka mu'amala ta masu neman jinsi daya na samun tirjiya daga alumma da ma hukumomi.

https://p.dw.com/p/3q69e
Afrika Homosexualität in Kenia
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

 Mutanen da ke wannan mu'amala na cin karo da tsangwama a wasu lokutan ma har ana kai musu hari, lamarin da ya kai su ga yin kira ga gwamnati da a mutunta 'yancinsu.

Alex Donkor ya kasance dan luwadi, kuma tun bayan da ya fito ya nuna wa duniya ga yadda ya ke a 2017, ya ke fama da tsangwama harma daga iyalansa da ya yi tunanin za su karbe shi. Yanzu haka dai Donkor ya bar mahaifarsa zuwa birnin Accra, saboda fargaba kasancewar duk wani nashi ya ki ya aminta da yadda yake, bayan haka ma harda barazana da rayuwarsa ta ke ciki.


"Idan mutum ya nuna wani cewa wancan na mu'amalar jinsi daya to za a iya kashe mutum har lahira. Abin da ke bani mamaki da alummar mu shi ne wane laifi mutum ya yi.  A kullum wannan shi ne halin da muke ciki ba ni kadai ba, hasali ma duk wanda ke cikin kungiyar nan ta LGBTQ rayuwarsa na cikin hadari a wannan kasa ta mu"


A cewar kungiyoyin kare hakkin bil'Adama kaso 40 cikin dari na yan kungiyar LGBTQ da ke kasar Ghana sun taba fuskantar hari. Donkor ya nuna damuwarsa game da yadda alumma kan iya nuna kiyayya karara a kan yadda wani mutum yake.


"Abin da ban takaici yadda wasu mutane ke nunawa wasu banbanci saboda kawai sun nuna cewar su ga yadda suke, kamar dai suma ba mutane ba ne, wannan abin takaicin ba wai a kaina kawai ya tsaya ba, a a akan su wadannan da ke nuna tsananin kyama wanda har sukan bar hakan ya kaisu ga cin zarafin wadannan mutanen".

 

A kasar ta Ghna dai ba a yarda da Mu'amala ta jinsi daya ba. Masu fafutukar samar musu yanci na cewar yanayin yadda ake nuna musu kyama ba zai canza ba a nan da dan karamin lokaci ba, saboda al'adu da ma adini  a cewar Goerge Lutterodt da ke zama malamin adinin kirista.

 

"Muna bin dokokin da mahukuntanmu suka shinfida mana, a nawa ra'ayin ina bin abin da gwamnati ta fada da kuma abin da doka ta ce da wanda al'adarmu ta nuna mana da ma wanda addinin kiristanci ya koyar da mu. A sabili da haka yan luwadi da yan madigo basu da wurin zama a cikin alummar mu"

Yanzu haka dai Alex Donkor da sauran yan uwansa da ke mu'amalar jinsi daya na fatan samun karbuwa a wajen jama'a nan bada jimawa ba abin da ake wa kallon da kamar wuya.