1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MƊD ta buƙaci Iran ta koma ga tattaunawa da hukumar IAEA

May 3, 2012

Manyan ƙasashen duniya sun nemi Iran ta warware taƙaddamar Nukiliyar ta da hukumar kula da makamashi ta duniya.

https://p.dw.com/p/14ooK
In this frame made from TV Herman Nackaerts, left, of the International Atomic Energy Agency, speaks to his team at the airport in Vienna, Sunday, Feb. 19 2012. A senior U.N. nuclear official said Sunday he hoped for progress in upcoming talks with Iran about suspected secret work on atomic arms, but his careful choice of words suggested little expectation that the meeting will be successful. The comments by Herman Nackaerts as his International Atomic Energy Agency team prepared to leave for Tehran for the second time in less than a month appeared to reflect IAEA reluctance to raise hopes that Iran will engage on an issue that it claims has no substance. (AP Photo / APTN) TV OUT
Ƙwararru daga IAEA zuwa IranHoto: dapd

A wannan Alhamis ce ƙasashe biyar dake da wakilci nai din-din-din a cikin kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya suka sanar da cewar tilas ne Iran ta amince da komawa ga tattaunawa tare da hukumar kula da harkokin makamashi ta duniya wato IAEA dake da hedikwatar ta a birnin Vienna na ƙasar Austria. A lokacin wani babban taron dake mayar da hankali akan yarjejeniyar hana yaduwar makaman ƙare dangin da ake yi a birnin na Vienna, ƙasashen da suka haɗa da China, da Amirka da Rasha da Faransa da kuma Birtaniya sun fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa dake cewar tilas ne Iran ta baiwa jami'an bincike na hukumar kula da harkokin makamashi damar zuwa ɗaukacin wuraren da ake zaton tana sarrafa sinadaran nukiliya. Wannan kiran dai ya zo ne kwanaki ƙalilan gabannin wani taron daya ƙunshi ƙasashen biyar da kuma Jamus a hannu guda game da ita Iran a ɗaya hannun, wanda birnin Baghadaza na Iraƙi zai karɓi baƙunci a ranar 23 ga watan Mayun nan, wanda ke da nufin tabbatar wa duniya cewar Iran ba ta da wata manufa ta ɓoye game da ƙera makaman nukiliya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas