Naɗa sabon shugaban IMF
May 18, 2011Ƙasar Amirka ta yi kira ga shugaban asusun ba da lamuni na duniya IMf, Dominique Strauss-Kahn da ya sauka daga wannan muƙami nasa. Sakataren kuɗin Amirka, Timothy Geitner ya ce akwai buƙatar gaggauta naɗa sabon shugaban asusun na riƙon ƙwarya har sai an tattance shari'ar da ake wa Strauss-Kahn. An ki bashi beli a 16 ga wannan wata ne bisa zargin da ake masa na cewa ya yi yuƙunrin yi wa wata mace fyaɗe. To amma ya musunta wannan zargi da wata ma'aikaciyar otel ta shigar yana mai cewa shi da ita basu gana ba. A ƙasar Faransa da yawa daga cikin shugabannin jam'iyyar Socialist da Stauss-Kahn ke jagoranta sun bayyanar da fushinsu game da yadda aka ta gabatar da shi a gaban 'yan jarida bayan da aka kama shi. A dai halin da ake ciki yanzu kafafen yaɗa labarun birnin New York sun ce ana sa ido akan Strauss Kahn a kurkukun da ake tsare da shi a wani tsibiri domin tsoron cewa mai yiwuwa ne ya halaka kansa da kansa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu