1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nahiyar Asiya da Iftila'in sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
April 23, 2024

Wani rahoton kungiyar kula da yanayi ta duniya ya ce ambaliyar ruwa da iska mai karfi suna daga cikin musabbabin iftilin da aka fuskanta a 2023.

https://p.dw.com/p/4f6LV
Ambaliyar ruwa a Indiya
Ambaliyar ruwa a IndiyaHoto: Prakash Adhikari/AP Photo/picture alliance

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce nahiyar Asiya ce ta fi fuskanta iftila'in sauyin yanayin da ya haifar da ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mace mace da hasara mai yawa na tattalin arziki.

Rahoton wanda aka yi wa lakabi da yanayin sauyin yanayi a Asia a 2023 da kungiyar kula da yanayi ta duniya ta fitar a yau talata ya ce ta'azzarar wasu muhimman lamuran muhalli suna da tasiri ga rayuwar al'umma da tattalin arziki da kuma tsarin zamantakewar hallitu da tsirai.