Masallatai da coci za su fara biyan haraji a Najeriya
August 18, 2020Wata sabuwar dokar kamfanoni ta kasar a Najeriya ta tanadi daukacin kungiyoyin addini da wuraren ibada a kasar su mika kansu a aske ga gwamnatin kasar da ke neman sauyin taku. Daga yanzu duk wani masallaci ko kuma coci za su biya haraji ga gwamnati.
To sai dai kuma dokar ta tayar da hankali a tsakanin shugabannin addinai da ke ganin mahukuntan kasar sun dauki hanyar kuntatawa malaman addini.
Pastor Yohanna Buru dai na zaman wani malamin addinin kirista a Kaduna da kuma yace dokar na zaman kokarin yakar addini a Najeriyar.
Akalla jamio'i masu zaman kansu guda 54 a tarrayar Najeriyar dai na zaman mallakin kungiyoyin addini na kirista a kasar bayan wasu guda biyu na yan uwansu musulmi, bayan kamfanoni da sauran cibiyoyi da ke tara kudi da sunan addinin.
Mallam Husaini Zakariya, wani malamin addinin musulunci ne wanda yace masallatai a Najeriyar basu da tsari na kasuwa face gudunmawa ta juma'a daga mabiya.
Sabuwar dokar dai ta dora kula da harkokin addinin a bisa hukumar rijistar kamfanoni wadda ta dora wa ikon rushe dukkan wata kungiyar addini ko kungiyoyin bada agaji a kasar, dokar da a cewar Barrister Buhari Yusuf ke zaman ruwan dare gama gari a ko'ina a duniya.
Abun jira a gani dai na zaman iya tantance tsakanin addinin da kasuwa cikin tarrayar Najeriya, kasar da malaman addini ke dada karfi na dukiya da ma tasiri a cikin harkokin al'umma na kasar.