1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ina rarar kudin mai suka shiga?

January 10, 2025

Ya zuwa karshen shekarar 2025 Najeriya na saran samun rarar da ta kai kusan triliyan 21 ko kuma kaso 40 cikin dari na kasafin kudin kasar sakamako na zare tallafin mai.

https://p.dw.com/p/4p2PJ
Thumbnail Business Beyond | Can anything challenge the almighty dollar's dominance
Hoto: Karel Navarro/AP Photo/picture alliance

Ministan kudin Najeriya Wale Edun ya shaida wa wani zaman bin bahasin kisan kudi na majalisar dattawa ta kasar cewar ba zai so yayi bayani a bainar jama'a ba bisa makomar kudaden.

Babban burin zare tallafin man tun daga farkon fari dai na zaman samar da kudade na ayyukan raya kasa da kila sake farfado da ababen more rayuwar da suka lalace.

To sai dai kuma ana kusantar shekaru biyu ba tare da kaddamar da hanya daya tilo ba, balle wani layin dogo ko kuma sabuwar tasha ta wutar lantarki ba.

Dr Yunusa Tanko kakakin jagoran adawar tarayyar Najeriya Peter Obi  kuma yace da walakin goron a miya.

Takardun kudin Naira na Najeriya
Hoto: Ubale Musa/DW

Wala wala da dukiyar al'umma, ko kuma tsarin kisan kudi, a kai da ta takarda ya zuwa yanzun dai rarar zare tallafin na iya biyan daukacin kudaden kasafin manyan ayyuka cikin kasar

Ibrahim Shehu sakataren kungiyar raya tattalin arzikin arewacin tarayyar Najeriyar yace daukaci na tambayoyin yan dokar na zaman mafi tasiri ga rayuwar miliyoyi cikin kasar.

Miliyoyi cikin kasar dai na biyan ninki kusan shida na farashin man da suke sha shekaru biyu baya a cikin neman mafitar matsin tattalin arzikin kasar.

To sai dai daga dukkan alamu an share shekaru biyun cikin fatan za ta yi kyau ga tattalin arzikin da ke karuwa a takarda, amma kuma aljihun yan kasar ke dada bushewa.

Hon Inuwa Garba dan jam'iyyar PDP ta adawa ne a majalisar wakilai ta kasar, yace a ka'idar aikin yan dokar na zaman dalla dalla na bayanan a cikin bainar jama'a maimakon a kuryar daki da masu mulkin na Abuja ke da bukata.

Gidan man NNPC a Abuja, Najeriya
Gidan man NNPC a Abuja, NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Komawa zuwa ga mai duka ko kuma ci gaba da tattalin arziki, duk da karuwar kudin shigar tarayyar da jihohi sakamakon zare tallafin man fetur, har ya zuwa yanzu dai batun cin bashi na zaman babbar hanyar tafiyarwar harkokin masu mulki a kasar.

Ya zuwa karshen shekarar 2025 dai ana saran samun rarar da ta kai kusan triliyan 21 ko kuma kaso 40 cikin dari na daukacin kasafin kudin tarayyar Najeriyar sakamakon zare tallafi.

To sai dai kuma daga dukkan alamu masu mulki na kasar na inda inda bisa makomar kudaden da ke zaman rara mafi yawa a tarihin kasar da kuma ke nuna alamun bin shanun sarki.

Ministan kudin kasar Wale Edun dai ya shaida wa wani zaman bin bahasin kisan kudi na majalisar dattawa ta kasar, cewar ba zai so yayi bayani a cikin bainar jama'a ba bisa makoma ta kudaden.

Babban buri na zare tallafin tun daga farkon fari dai na zaman samar d akudade na aiyyukan raya kasa da kila sake farfado da ababe na more rayuwar dake lalace.