1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan tsaro gabanin baiyana sakamakon zabe

Uwais Abubakar Idris RGB
February 24, 2019

Hukumar zabe ta INEC na shirin fara karbar sakamakon zabe, inda tuni jami'an tsaro suka toshe daukacin hanyoyin shiga cibiyar gabanin soma karbar sakamakon zabe daga jihohi

https://p.dw.com/p/3E0YW
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Hukumar zabe mai zaman kanta  ta ce sakamakon zaben jihar Eikita na kan hanya zuwa Abuja domin bayyanar da shi a daren wannan Lahadi. Yanzu hakula sun koma kan hukumar zaben inda Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ya ce a yanzu ana tattara sakamkon zabe a matakan kanana hukumomi, yayin da na jihar Ekiti ya kamala.

Tun da farko, shugaban hukumar zaben ya ce hukuma ba ta ji dadi ba a kan yadda aka samu tashin hankali da ya hana mutane yin zabe a wasu yankuna na Najeriyar, abinda ya sanya ake sake zaben a Lahadin nan a mazabun da ke jihohin Abia, da Bayelsa da Benue da Plateu da Zamfara da kuma Sokoto da yankin Kuje da ke Abuja.

Baya ga wannan ma dai ya musanta labarin cewa an soke zaben wasu jihohi. A game da masu yada sakamakon zabe ta kafofin sada zumunta kuwa, shugaban hukumar zaben ya ce hukumar ce kadai ke da hurumin bayyana sakamakon zaben. A yanzu kalo ya koma sama inda alummar Najeriya da ma kasashen waje ke jiran fitar da cikakken sakamakon zaben na Najeriya domin jin ko wanene zai zama sabon shugabanta na wani wa'adin shekaru hudu masu zuwa.