1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Soji za su kare jirgin kasa daga hare-hare

November 12, 2021

Sakamakon barazanar tsaron da ke neman durkusar da sufurin jirgin kasa a tarrayar Najeriya, rundunar tsaron kasar ta kaddamar da shirin shawagi da jiragen sama kan layin da ya hade Kaduna zuwa Abuja da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/42wGT
Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Hoto: DW/U. Musa

Jirgin kasa da ke zama takamar 'yan bokon arewacin tarrayar Najeriyar ya fuskanci jerin hari har guda biyu a tsakanin 20 ya zuwa 21 ga watan Oktoban 2021, lamarin da ya tada hankali masu mulki da talakawan yankin da ke masa kallo a matsayin damar kauce wa barayin dajin da suka dauki dai dai.

Sai dai rundunar sojan kasar ta ce ta fara wani shirin tura jiragen sama da nufin shawagi kan layin dogon da ke da tsawon kilomita kusan 200 da kuma ke zaman irinsa na farko na zamani da Najeriya ta kaddamar. Duk da cewar ba bayani dalla-dalla na yawan jirage da lokacin shawagin dai, ana kallon matakin a matsayin kokari na karfafa gwiwar matafiya da dama suka koma kan tituna bayan harin da ya tada hankali. Matafiya da dama ciki har da Isma'il Yufu sun kaurace wa layin dogon bayan harin da ya kai ga jefa bam a kan layin ko bayan harbin matukin jirgin.

Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna Präsident Buhari
Shugaba Buhari ne ya jagoranci bikin bude layin jirgin Abuja zuwa KadunaHoto: DW/U. Musa

Ko bayan layin jirgi na Kaduna zuwa Abuja dai, Najeriya na da wasu layukan guda biyu da suka hade Lagos da Ibadan ko bayan Itakpe zuwa Warri, da kuma dukkaninsu ke jidon kaya da mutane. Akwai tsoron cire imani kan sufurin na iya kai kasar zuwa baya a cikin sabon shirin amfani da jiragen kasa da nufin sauya tattalin arzikin tarrayar Najeriyar. Wannan shirin da ya lamushe dubban miliyoyin daloli, amma kuma har yanzu yana tsumman goyo. Group Captain Sadeeeq Garba Shehu da ke sharhi kan tsaro a tarrayar Najeriyar ya ce batun rashin isassun jiragen na iya kawo cikas cikin shirin mai tasiri.

Rashin isassun jiragen dai na zaman ummul aba'isan tsawaitar rashin tsaron tarrayar Najeriya, kasar da ke tinkarar manyan matsaloli na ta'adda da na barayin daji da jiragen da yawansu bai wuce 100 ba.