Bukukuwan Kirismeti babu armashi saboda corona
December 24, 2020A bisa al'ada dai tun ma kafin sallah a kan samun karuwar hada-hadar jama’a a kasuwani da tashoshin mota domin wadanda ke son tafiya don gudanar da bikin tare da ‘yan uwa da abokan arziki. To sai dai a bana abubuwa sun canza sosai inda babu irin wannan cukunso a mafi yawan tashoshin motar da ke Abuja. Kasuwani da aka saba samu sun tsinke a bana an ga canji na raguwar masu kai da kawo musamman ma dai mata.
Koma bayan tattalin arziki da corona sun yi tasiri wajen rage armashin bukukuwan na Kirismeti a Najeriya
Koma bayan tattalin arziki da Najeriyar ta sake afkawa a ciki dai babban matsala ce ga harkokin yau da kullum a kasar musamman masu karamin karfi da yanayin ya kara jefa su a cikin hali na ‘yan rabana ka wadatamu. Malam Yusha’u Aliyu masani harkokin tattalin arziki a Najeriyar ya bayyana dalilan na tattalin arziki da suka ragewa bikin Kirismetin armashi da cewar babban kalubale ne ga kasar. Pastor Yohana Buru shugaban Cocin Evengelical ne da ke Kaduna: ''Ba da umurnin rufe wuraren shakatawa da klob-klob a Abuja da gwamnati ta yi saboda karuwar cutar Covid 19 da ya fado a wannan lokaci ya ragewa bukukuwan armashi musamman a tsakanin matasa da suka saba ziyaratar wadannan wurare a lokacin hutu.''