1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na bincike kan tsere wa biyan haraji

November 8, 2017

A kokarinta na neman gano gaskiyar lamari bayan bankado sabuwar badakalar nan ta Paradise Papers, gwamnatin Tarrayar Najeriya na bincike da nufin tabbatar da gaskiya domin daukan mataki.

https://p.dw.com/p/2nIhb
Baba Cartoon Paradise Papers Nigeria
Hoto: DW/Baba

Kama daga Panama Papers ya zuwa ga batu na Paradise Papaers dai, daga dukkan alamu gugguwar da ke kadawa a cikin Tarrayar Najeriya na zaman ta boye kudade a banagren 'yan boko da a baya a ke zargi da karkatar da akalar kudaden kasar ya zuwa cibiyoyin boye kudi iri-iri a duniya. Wannan bincike na hadin gwiwar 'yan jaridu masu bincike ya ambato kama daga masu takama da siyasa ya zuwa manyan jami'an bankuna inda aka ce sun boye tsabar kudi kusan Triliyan goma na dalar Amurka da nufin kaucewa biyan haraji.

Nigeria Symbolbild Korruption
Dubban Nairori ne 'yan Paradise suka ki biyan harajinsuHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Duk da cewar har ya zuwa yanzu ba a kallonsa a matsayin aikin laifi ga mazauna fadar gwamnatin ta Najeriya, ma'aikatar kudin kasar ta ce ta kaddamar da bincike kan masu ruwa da tsaki da kudaden da nufin tabbatar da kaiwa ga halacinsu, sannan da cika ka'ida ta harajin da ke zaman batutuwan da kasar ta sa wa gaba. Koma ya take shirin kayawa a tsakanin masu kokarin boye kudaden da kuma masu neman kudin ido rufe dai, daga dukkan alamu mutanen da suka mallaki miliyoyin dalolin ka iyaya fakewa da sabon shirin afuwar gwamnatin kasar da ya tanadi fitowa fili tare da bayyana yawan dukiya da kuma biya mata haraji inda kuma gwamnatin za ta yafe tsohon bashin harajin.