1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Siyasar jihar Kano na fama da rudani

Nasir Salisu Zango MA
May 16, 2022

Yayin da zabukan 2023 ke matsowa, guguwar sauyin sheka a jam'iyyar APC da rashin tabbas ga jam'iyyar PDP na ci gaba da kawo rudani a siyasar jihar Kano a Najeriya.

https://p.dw.com/p/4BNh0
Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar KanoHoto: Salihi Tanko Yakasai

Fadi in fada gami da tsallen tsuntsu daga bishiya zuwa bishiya baya ga jifan juna da bakaken kalamai, su ne muhimman batutuwan da a yanzu suka zama gajimaren da ya lullube siyasar jihar Kano. Yanzu haka dai jam'iyyar APC mai mulkin jihar na cewar galiban masu kaurace mata sun fara yin kome, ungulu tana komawa gidanta na tsamiya.

Alhaji Ahmed Aruwa shi ne darektan yada labarai na jam'iyyar a Kano, ya ce da ma siyasa ta gaji haka kuma jiga-jigan da suka bar jam'iyyar sun fara dawowa har ma ya ce tuni Sanata Barau Jibril na kano ta Arewa ya mayar da wukarsa cikin kube, saboda an daidaita da shi. Haka ma ya ce yanzu haka ma suna kokarin sulhuntawa da Sanata Ibrahim Shekarau, wanda shi ma tuni ya nade kayansa domin barin jam'iyya.

Karikatur Nigeria/Kano APC Krise

Shi ma Honorabul Musa Iliyasu Kwankwaso guda daga cikin na hannun daman gwamna Ganduje, na da ra'ayin cewar da ma siyasa haka ta gada, kuma shi ma ya hakikance da cewar wadanda suka tafi suna kan hanyar dawowa. Hononorabul Murtala Kore shi ne dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Danbatta kuma guda daga cikin wadanda suka ayyana barin APC amma daga baya suka ce sun daidaita sun dawo, ya ce tangarda aka samu amma yanzu komai ya daidaita

Daga bangaren magoya baya, masu fashin baki kan siyasa irin su Abubakar Ibrahim na da fasalin cewar lissafin siyasar Kano a yanzu kan mutane uku take, wadanda su ne shika-shikan fayyace siyasar jihar.

A kowane lokaci daga yanzu za a ji matsayar Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa, wanda matsayin su ne zai fayyace ainihin alkiblar siaysar Kano a wannan lokaci. Wannan ne ma ya sa kowane bangare tsakanin Kwanwkaso da Ganduje ke kokarin jawo malamin zuwa wurinsu, a waje guda kuma jam'iyyar PDP ta shiga mummunan yanayi na rashin tabbas, kasancewar shugabannin da ke rike da akalarta a yanzu masu imani da akidar tafiyar kwankwasiya ne, lamarin da ke nuna yadda jam'iyyar ke cikin halin kila wa kala.