1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta ce shugaban sojojin kasa na raye

October 21, 2024

A Najeriya al'umma na ci gaba da aza yar tambaya a kan makomar shugaban sojin kasa Laftanar janar Toareed Lagbaja inda ya shafe sama da makonni biyar a wajen kasar.

https://p.dw.com/p/4m4J9
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya Hoto: AUDU ALI MARTE/AFP/Getty Images

Wasu dai sun ce yai nisa a barzahu, wasu kuma suka ce ya zi magana da shugaban kasar, a yayin kuma da wasu ke fadin ya ma sha koko da kosai, duk a cikin labarin Laftanar Janar Taoreed Lagbaja da ke zaman babban hafsan sojan kasa na Tarayyar Najeriya.

Lagbajan da ya sa kafa ya bar Najeriya dai ya shiga rudani bayan da aka yi masa kallon karshe cikin gidan sojojin a farkon watan jiza na Satumba. Daukacin gidan sojojin dai sun share tsawon lokaci suna ta kokari na kwantar da hankula bisa makomar babban hafsan da ke zaman na kan gaba cikin gidan sojojin na kasa.

Ko da ranar yau Litinin dai shi kansa babban hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa ya gana da shugaban Najeriya Bola Tinubu kuma daga dukka na alamu bisa makomar hafsan da ke jagorantar yakin rashin tsaron kasar a halin yanzu.

Nigeria | Offiziere der nigerianischen Armee | Archivbild
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

To sai dai kuma batan Lagbajan da ya share makonni guda biyar a baya na fage dai na jawo ka-ce na-ce cikin kasar da ke da tsohuwar al'adar boye lafiya ta shugabanni a cikin yanayin rudu. Duk da cewar dai can cikin gidan sojojin sun bayyana mai tafi da harkokin rundunar sojan na kasa, ana kallon batan Lagbajan da idanu daban-daban a kwararru daban cikin gidan sojojin.

Wing Commander Musa Isa dai wani tsohon jami'i a rundunar sojojin da kuma ya ce rashin ganin Lagbajan a bainar jamaa, bai saba da ka'idar gidan sojojin ba. Kama daga boko ta haramun zuwa ga barayin dajin da ke a arewa maso yammacin kasar dai sojan na kasa ne ke jan ragamar kokari na kwantar da hankula a Najeriya a halin yanzu.

Ana kuma kallon batan Lagbajan na iya shafar kwarin gwiwar dubban sojojin da suke a filin daga cikin kasar da ma a wajenta. Ya zuwa yammacin yau din nan dai rundunar tsaron kasar ta ce babu shugaban riko cikin gidan sojoji na kasan.