1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yajin aikin malaman jami'o'i

November 17, 2016

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya wato ASUU na ci gaba da yajin aiki, lamarin da ya jefa dalibai cikin halin rashin tabbas tare da kawo cikas a harakar ilimin kasar, wacce dama take fuskantar kalubale.

https://p.dw.com/p/2SrLD
Nigeria Bayero Universität in Kano
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/GettyImages


A Najeriya ana ci gaba da yajin aikin gama gari da malaman jami’o'in gwamnati suka shiga a kasar, inda lamarin ya gurgunta daukacin karatu a wadannan jami’o'i. Al’amura sun tsaya cik a jami’ar Abuja, inda dalibai ke ci gaba da watangaririya saboda hali na rashin tabbas da suka shiga dalilin yajin aikin. Kalilan daga daliban da suka rage dai na jiran tsammani. Matsalar dai tafi muni ga sababbin daliban da suka zo daga nesa domin kokarin yin rijista, wadanda aka barsu suna ta watangaririya kamar yadda Precious Zachariah dalibar da ta zo daga jihar Adamawa don rijistar fara karatu tke cewa:

 

" Mun zo makaranta don yin rijista kuma gashi ana yajin aiki. Don haka muna kira ga gwamnati da ta ji kukan kungiyar malaman ta share masu hawayensu ko ma samu mu yi rijista domin kama karatu."

Nigeria Studenten in Jos
Hoto: picture-alliance/epa/Ruth McDowall

 

Yawaitar shiga yajin aiki ga malaman jami’oi na Najeriya dai babbar matsala ce a cikin kasar da sannu a hankali ke kara shafar darajar ilimi a makarantu wadanda dama can ake kukan sukurkucewarsa. Abin da ya sanya  daliban Najeriya ci gaba da turuwa zuwa kasashen waje da ba su kai Najeriyar ba. Malam Faruq Musa ma’aikacin jami’ar Abuja ne a sashin da ba na koyarwa ba ya bayyana damuwarsu a kan kwan-gaba-kwan-baya na harkar ilimin jami’a a Najeriyar:

 

" Hadarin da ke tattare da yajin aikin malaman jami'a shi ne jami'ar a kullum za ta ja da baya ne a maimakon ta ci gaba. Idan yau aka ce an tafi yajin aiki na mako daya to fa duk wani aiki na koyarwa an dakatar da shi kenan. Tsarin jadawalin karatun an birkita shi. Ka ga wannan dole ya shafi martaba da darajar ilimi, musamman 'ya'yan talakawa wadanda ba sa iya fita waje su biya su yi karatu."

Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano
Hoto: DW/N. S. Zango

 

A yayinda ake ci gaba da kokari na shawo kan malaman su janye yajin aiki na gargadi da ka iya zarcewa zuwa lokaci mai tsawo, ga Mr Livinus Akong dalibi da ke karatun likita a jami’ar Abuja na cike da fatan za a samu sasantawa:

 

" To ni ban san wajen da matsalar take ba illa kawai, fatana shi ne a sasanta malamai su fara koyar mana da karatu."


A yayin da ake can ake ci gaba da tattaunawa ana cike da fatan samun sasantawa a yajin aikin.