1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya; 'Yan adawa na neman a soke zabe

Uwais Abubakar Idris MAB
February 28, 2023

Kungiyoyin fararen hula da wasu jam'iyyun adawa sun gudanar da zanga-zanga a wasu sassan birnin Abuja, inda suke kira da soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga wannan wata.

https://p.dw.com/p/4O5Xd
'Yan takarar shugaban kasa a Najeriya: Peter Obi, Bola Tinubu, Atiku Abubakar Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Masu zanga-zangar da suka zo har kusa da cibiyar da ake tattara sakamakon zaben shugaban kasar sun nuna bukatar a dakatar da sanar da sakamakon zabe, tare da neman a kori shugaban hukumar zabe ta Najeriyar Farfesa Mahmood Yakubu. Daga cikin kungiyoyin da suka gudanar da wannan zanga-zanagr ta lumana, har dai kungiyoyin fara hula da suka hada da Concerned Nigeria da ta votes Count.

Sai dai shugaban hukumar zaben ta Najeriya ya ci gaba da karbar sakamakon zaben, inda ya ce akwai jihohi 17 da suka iso da sakamakonsu, abin da ke nuna yiwuwar kammala aikin tare da sanar da wanda ya lashe zaben na Najeriya.

Mr Oseloka Obaze na cikin wadanda suke kiran a soke zaben na shugaban kasar Najeriya, inda ya ce: ‘' Akwai abubuwa na tada hankali da sai dai kawai a dangantasu da hukumar zabe, don haka ba za mu amince da su ba, wannan ya sa a rusa zaben kawai a sake sabo, domin wannan ne zai daidaita al'ammura, kuma in ba'a yi haka ba, zai sa mutanen da aka zaba su bi kan titi suna zanga-zanga, mu dai muna kiran a zauna lafiya''.