1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta ba da tukwicin Naira miliyan 50

May 7, 2014

Mahukunta a tarayyar Najeriya sun yi tayin ba da ladar dalar Amirka dubu 300 ga wanda zai ba da labarin wurin da 'yan matan nan da aka yi garkuwa da su a Chibok suke.

https://p.dw.com/p/1BvD1
Nigeria Polizei in Abuja
Hoto: Reuters

Rundunar 'yan sandar Najeriya ta yi tayin ba da ladar Naira miliyan 50 wato kwatankwacin dalar Amirka dubu 300 ga duk wanda zai ba da sahihin labarin da zai kai ga ceto dalibai 'yan matan nan fiye da 200 da wasu 'yan tawayen Musulmi suka sace. Garkuwar da kungiyar Boko Haram ta yi wa 'yan matan daga wata sakandare dake garin Chibok na jihar Borno ta sha suka da zanga-zanga daga a sassa daban daban na Najeriya, tare kuma da matsin lamba kan gwamnati ta ceto 'yan matan. Hushin jama'a ya karu bayan da a ranar Talata aka samu labarin yin garkuwa da wasu 'yan matan a wani kauye da ke a jihar ta Borno. Yanzu haka dai gwamantin Najeriya ta karbi tayin Amirka na tura jami'an tsaronta don taimakawa a ceto 'yan matan wadanda shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi barazanar sayar da su a matsayin bayi. Tabarbarewar tsaro a Najeriya ta mamaye taron tattalin arzikin duniya a kan Afirka da ake yi a Abuja a wannan mako.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu