1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shimfida bututun gas daga Najeriya zuwa Turai

Gazali Abdou Tasawa ZUD
July 29, 2022

Rikicin Ukraine da ya haifar da bukatar iskar gas a Turai ya sanya kasashen Najeriya da Nijar da Aljeriya farfado da wannan tsohuwar yarjejeniya. Ministocin makamashin kasashen ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

https://p.dw.com/p/4Et3i
Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Tun a shekara ta 2009 kasashen uku suka kaddamar da shirin mai suna Projet Gazoduc Transsaharien ko Trans-Saharan Gas Pipeline. Shirin ya tanadi shimfida bututu domin fitar da Iskar gas din Najeriya zuwa Turai domin sayarwa.Bututu mai tsawon kilomita 4,128 ne zai ratsa Najeriya da Nijar har zuwa kasar Aljeriya, inda zai jona ga bututun jigilar iskar gas na Aljeriyar zuwa Turai. Sai dai tun daga wancen lokaci batun ya zamo shafa labari shuni. To amma tsohon ministan fetur na Nijar Injiniya Maman Lawan Gaya  ya ce bukatar makamashin da Turai ke da ita sakamakon rashin fahimtar da suke samu da Rasha biyo bayan yakin Ukraine ce ta sanya kasashen na Afirka farfado da tsohon shirin.  

Tunesien 2022 | Erdgas-Pipeline
Hoto: Fethi Belaid/AFP/Getty Images

To ko wani alfanu kasar Nijar za ta iya samu a cikin wannan shiri na shimfida batutun zuwa Turai? 

''Ratsawar kadai da bututun zai yi ta Nijar, kasar za ta iya samun akalla miliyan dubu daya na CFA a duk shekara. Sannan Nijar za ta samu abin da za ta iya yin takin zamani da kuma sarrafa roba. Kazalika za a gina masana’antu da samar da ayyuka ga injiniyoyi da jami’an tsaro domin kula da bututun a Nijar.'' in ji Injiniya Lawan Gaya

Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

To sai dai a nata bangare kungiyar Rotab mai sa ido kan aikin hakar ma’adanai a Nijar, ta bakin daya daga cikin shugabanninta, Malam Ilyassou Boubacar, kira ta yi ga gwamnatin Nijar da ta kula da ganin an kiyaye muhalli a cikin aikin.

An kiyasta cewa aikin gina wannan bututun zai lakume kudi miliyan dubu goma na dalar Amirka. Sai dai kawo yanzu kasashen uku ba su sanar da lokacin soma wannan aiki ba da lokacin kammala shi.