1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala atisayen jinjina karfin sojan kungiyar NATO

June 23, 2023

Kungiyar tsaro ta NATO ta kammala atisayen sojojin sama na kwanaki 10 da ta gudanar da nufin jinjina karfin sojanta a gabashi da kuma tsakkiyar Turai inda ake fama da barazanar daga Rasha.

https://p.dw.com/p/4SzXE
Jirgin yakin NATO yayin atisayen sojojin sama a Jamus
Jirgin yakin NATO yayin atisayen sojojin sama a JamusHoto: Marcel von Fehrn/Eibner-Pressefoto/picture alliance

Atisayen da aka yi wa take ''Air Defender 23'' ya gudana ne a karkashin jagorancin kasar Jamus, sannan kuma ya samu halartar sama da sojoji dubu 10 tare da jiragen yaki 250 daga kasashe 25 mambobi da kuma masu zawarcin shiga kawancen ciki har da Japan da Sweden.

Bayan kammala atisayen da ke zama na farko mafi girma a tarihin kawancen na NATO, ministan sufurin kasar Jamus Volker Wissing, ya yaba da yadda aka karkare ba tare an samu wani tsaiko a bangaren zirga-zirgar jiragen sama ba.

Jakadiyar Amirka da ke Jamus Amy Gutmann, cewa ta yi atisayen babban sako ne zuwa ga Rasha da kawayenta, tare da nuna cewa kasashen Turai suna iya kare kansu daga duk wata barazana.