NATO fordert Taten von Russland
June 26, 2014Ministocin harkokin wajen na NATO dai sun jingine Agendar taronsu na watan Satumba, dama sauran batutuwa dangane da sharar fagen wannan taro da suke shirin gudanarwa nan da 'yan watanni bisa ga al'ada. A maimakon hakan hankalinsu ya koma kan rikicin Ukraine da kuma yadda za su bullowa Rasha kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya tabbatar;
" A yanzu duniya ta sauya daga yadda take a baya. Ba za'a nuna halin ko oho dangane ko wane irin batu ba. Bamu da wani karamin lokaci kuma wata kila ma bamu da matsakaicin na daukar mataki".
Kawo wannan lokaci dai Moscow bata fito fili ta yi wani abunda ya taka kara ya karya ba dangane da rikicin na Ukraine tun watan Maris, koda kuwa a matsayinda la abokiyar huldar NATO ko kuma sabanin haka. Bisa dukkan alamu dai ci gaban wannan rikici na barazanr haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin kasarshen Turai. Sai dai bai kamata a koma yanayi irin na zamanin cacar baka ba, kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya fadawa 'yan jarida;
" Mu na cikin wani yanayi ne na nazarin rikicin kasar Ukraine, yanayin da aka yi watsi da yarda. Yanzu ya ragewa Rasha ta sake farfado da wannan yarda akan sabon tubali, ta inda za'a samu tattaunwa a mataki na ministoci tsakanin NATO da Rashan".
Ministan harkokin wajen na Jamus wanda ya bar Ukraine ranar Talata, ya fadawa takwarorinsa na Turai a birnin na Brüssels irin yanayin daya samu kasar a ciki. Ministocin kungiyar tsaro ta NATOn dai sun yi maraba da matakin da majalisar dokokin Rasha da shugaban kasar suka dauka na janye sojojinsu daga kan iyakar Ukraine, wanda suka bayyana da zai rage tayar da jijiyar wuya a yankunan gabashin kasar. Duk da cewar murna ta koma ciki dangane da wannan fatan, tun bayan da 'yan awaren gabashin Ukraine suka kakkabo jirgin sojin gwamnati.
Ministan harkokin wajen Ukraine Pavlo Klimkin wanda ya halarci taron na ministocin NATO, ya bayyana manufar gwamnati na aiwatar da tsarin samar da sulhu wanda shugaba Petro Poreshenko ya gabatar:
" Irin wannan tsokana na da hatsari sosai musamman dangane da aiwatar da shirin tsagaita wuta. A namu bangare muna yin iyakar kokarinmu na ganin cewar raguwar kazancewar rikicin yankin Donesk domin abun ya yi tsanani".
A lokacin taron dai, ministan harkokin wajen Jamus da na Ukraine sun tattauna ta wayar tarho da takwaransu na Rasha Sargei Lavrov. Bangaren Jamus din dai na muradin ganin an fadada yarjejeniyar tsagaita wuta da wa'adinsa ke karewa a wannan Juma'ar.
Babban sakataren NATO Anders Fogh Rasmussen ya yi kira ga Rasha da ta yi amfani da matsayinta wajen rage radadin da ake fama da shi a gabashin Ukraine;
" Muna kira ga Rasha da ta ci gaba da janye dakarunta dake kan iyakokin Ukraine. Kazalika ta dakatar da kwararar makamai ta kan iyakokinta, a lokaci guda kuma akwai bukatar ta yi amfani da kimar da take dashi a idanun 'yan awaren, wajen ganin cewar sun ajiye makamansu tare da kawo karshen wannan rikici".
Ministzocin harkokin wajen na NATO ciki har da Amurka dai sun cimma matsaya na ci gaba da tursasawa Rasha kan shawo kan rikicin 'yan awaren na Ukraine, sai dai babu sabon takunkumi da suka dora mata.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe