1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na kira da a kai dauki wa Ukraine

June 8, 2023

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya yi kira ga kasashen kawancen su gaggauta kai dauki ga al'ummar Ukraine da ambaliyar ruwa ta daidaita.

https://p.dw.com/p/4SM3b
Barnar da ambaliyar ruwa ke yi a Ukraine
Barnar da ambaliyar ruwa ke yi a UkraineHoto: Vladyslav Musiienko/REUTERS

Kwanaki kadan bayan gagarumar ambaliyar da ta yi barna a birane da kauyukan kudancin Ukraine bayan harin da aka kai wa wata madatsar ruwa, Sakataren kungiyar tsaro ta NATO ya bukaci kasashe membobin kawancen kungiyar da su hamzarta kai wa wadanda abin ya shafa dauki.

Jens Stoltenberg, ya yi wannan kira ne a yayin taron jakadun kasashe 31 na NATO da aka gudanar bisa bukatar hukumomin Kiev don duba halin da al'ummar yankunan kasar suka shiga kwanaki kadan bayan ambaliyar da ke ci gaba da haddasa asara.

Shi ma babban jami'in diflomasiyyar Ukraine Dmytro Kouleba, da yake magana ta kafar bidiyo a yayin taron, ya yi bitar adadin barnar da ambaliyar ta haddasa, ya kuma gabatar da jerin bukatun kasar don taimakawa wadanda lamarin ya ritsa da su.