Ukraine za ta samu tallafin NATO
November 29, 2022Talla
Ministocin kula da harkokin ketare na kasashen da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO, sun taru a birnin Bucharest na Romeniya a wannan Talata domin tattauna hanyoyin da za su ci gaba da tallafa wa Ukraine.
A jawabinsa na bude taron, Jens Stoltenberg, sakatare-janar na kungiyar ya ce NATO ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin fitar da Ukraine daga halin da take ciki. Stoltenberg ya ce babu gudu ba ja da baya, ministocin za su tabbatar Rasha ba ta yi nasara a kan Ukraine ba.
Tun kafin a fara wannan taro dai sakatare janar na NATO din ya yi zargin cewa Rasha na amfani da arzikin makamashi da take da shi a matsayin makami musamman a yanzu da aka shigo lokacin hunturu a Ukraine da kasashen Turai.