NATO na waiwaye kan cika shekaru 75 da kafuwa
April 4, 2024A taron da ake gudanarwa a birnin Brussels na kasar Belgium, ministocin harkokin wajen zasuyi waiwaye kan daftarin da aka rattabawa hannu na kafa kungiyar NATO a birnin Washington na kasar Amurka, a ranar 4 ga watan Afrilun 1949.
Karin bayani: NATO za ta ci gaba da ba Ukraine makamai
Sakatare Janar na kungiyar Jens Stoltenberg, ya ce zasu ci gaba da aiki tare wajen karfafa alakar da ke tsakanin kasashe mambobin kungiyar kuma zasu ci gaba da aiki da kawayen kungiyar domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Karin bayani: Sweden ta zama memba na 32 na kungiyar NATO
Kungiyar ta fara da mambobi 12 har zuwa 32, kasashen da suka shiga kungiyar ta NATO a baya bayannan sun hadar Sweden da Finland da suka shiga kungiyar domin jaddada goyon baya ga Ukraine tun bayan farmakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine a 2022.