1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kungiyar NATO ta gargadi kasar Rasha

Abdoulaye Mamane Amadou
November 15, 2021

Kwanaki bayan da Rasha ta jibge dakarun tsaronta a iyaka da Ukrain, kungiyar tsaro ta NATO ta gargadi kasar, a yayin da Jamus ta bukaci Rashar ta nuna dattako.

https://p.dw.com/p/431Rc
Russland Yelnya | Satellitenbild | Russisches Militär
Hoto: Maxar Technologies/AFP

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya yiwa Rasha hannunka mai sanda game da abinda ya kira sabuwar barazana da kasar ke yi kan iyakatarta da Ukrain.

Mr. Stoltenberg ya ce sabuwar tsokanar da Rasha ke yi ta hanyar jibge dakarunta kan iyakar Ukrain abu ne mai tayar da hankali ko baya ga zama wata babbar barazana, saboda hakan yana kira ga kasar da ta fayyace aiyukanta na soja a yankin.

Ita ma kasar Jamus ta nuna matukar damuwa game da batun sojojin na Rasha a iyakar Ukrain, tana mai cewa yana da kyau Rahsar ta nuna dattaku, a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus.