1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na fatan sasanta Rasha da Ukraine

Abdul-raheem Hassan MAB
January 10, 2022

Washington na fatan kawar da hatsarin sabuwar mamayar da ake zaton Rasha za ta yi wa Ukraine, Amirka ta fadi haka ne yayin fara tattaunawar masu shiga tsakani a rikicin Moscow da Kiev da aka fara a birnin Geneva.

https://p.dw.com/p/45LWQ
Beljiyam I Jens Stoltenberg I NATO
Babban sakataren kungiyar NATO, Jens StoltenbergHoto: Johanna Geron /REUTERS

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce yana fatan tattaunawar za ta samar da hanyar warware rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, amma ya gargadi Rasha ta kuka da kanta, idan ta sake kai wani hari kan Ukraine.

"Ina maraba da taron da zai gudana a yau, da kuma wanda za a yi a tsakiyar mako. Amma ba na tsammanin tarukan za su warware dukkan batutuwan. Abin da muke fata shi ne, mu amince a kan hanyar da za a bi, mu amince kan jerin tarurrukan da za a yi, mu amince kan tsari. Don haka bana ganin tarukan da aka tsara za su magance matsalolin."