1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta matsa wa Putin lamba kan Ukraine

Mouhamadou Awal BalarabeMay 13, 2015

Kasashen da ke da kujera a cikin kungiyar Tsaro ta NATO sun nemi shugaba Putin na Rasha ya daidai tsoma baki a rikicin gabashin kasar Ukraine

https://p.dw.com/p/1FPUp
Hoto: NATO

Kasashen yammacin duniya na ci-gaba da matsa wa Rasha lamba domin ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma akan rikicin gabashin Ukraine. Cikin wata sanarwa da suka wallafa bayan taron da suka gudamar a birnin Antalya na Turkiya, kasashe 28 da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO sun bukaci Moscow ta daina tsoma bakinta a harkokin cikin gida na Ukraine.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry wanda ya gana da Vladimir Putin a jiya Talata, ya bayyana wa takwarorinsa na NATO cewa shugaban na Rasha ya nuna alamun mika wuya ga bukatunsu. Kasashen na yammacin duniya na neman a aiwatar da daukacin fannonin da ya yarjejeniyar birnin Minsk ta tanada, ciki kuwa har da janye daukacin makamai a yankin na Ukraine da ke fama da rikicin aware.

Mutane dubu shida da 200 sun rasa rayukansu a gabashin Ukraine tun baya barkewar rikici tsakanin dakarun gwamnati da kuma masu neman dara kasar gida biyu.