NATO ta nemi a bar Finland da Sweden zama mambobinta
February 28, 2023Jens Stoltenberg da ya yi wannan kira a birnin Helsinki na kasar Finland, ya ce yanzu ne dai-dai lokacin da ya kamata kasashen na Turkiyya da Hungary su sauko daga kujerar naki da suka dare domin ganin an sami maslaha a korafe-korafen da suke hana ruwa gudu.
Tun a watan Mayun shekarar da ta gabata ne bayan mamayar Rasha a Ukraine, kasashen biyu na Finland da Sweden a hukumance suka mika takardar neman shiga kungiyar tsaron, sai dai bukatun nasu ya ci karo da turjiya da yanzu haka ake fatan magance ta.
Stoltenberg ya ce duka kasashen biyu sun cika sharudan da aka cimma da Ankara, Sai dai a nata bangaren Ankara ta ce har yanzu Sweden ba ta kai ga cika wadannan sharuddan ba.
Ana dai ganin akwai alamun nasara a bangaren Turkiyya tun bayan sanarwar da ta yi na yiwuwar ci gaba da tattaunawa a ranar 9 ga watan Maris da za mu shiga.