An gargadi Rasha kan kera makaman kare dangi
February 12, 2019Talla
Babban magatakardar na kungiyar tsaron, Jens Stoltenberg ne ya fadi hakan a wannan Talata, ya kara da cewa, kungiyar ta NATO a shirye ta ke ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kare yankin Turai amma duk da haka akwai bukatar a sassanta. Cikin watan Oktobar bara ne, Shugaba Donald Trump ya sanar da cewar kasar za ta yi watsi da yarjejeniyar makaman matukar Rasha ta ki bin umarnin kungiyar tsaron ta NATO kan sababbin makaman masu linzamin da ta kirkira.
A gobe Laraba ministoci a karkashin kungiyar za su yi wata ganawa ta kwanaki biyu a birnin Brussels don yin nazari kan sabbin matakan tsaro don kare yankin daga barnar da ake gudu makaman na Rasha ka iya haddasawa yankin Turan.