1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta tura karin sojoji zuwa Kosovo

Abdullahi Tanko Bala
May 30, 2023

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO na shirin tura karin sojoji 700 don karfafa rundunar kiyaya zaman lafiya ta KFOR a Kosovo.

https://p.dw.com/p/4Rz10
Kosovo, Zvecan | Polnische KFOR-Soldaten stehen Wache
Hoto: Ognen Teofilovski/REUTERS

Wannan ya biyo bayan shafe kwanaki ana tashin hankali da ya yi sanadiyar jikata sojojin KFOR 30 yayin da suke kokarin kawar da masu zanga zanga daga gine-ginen gwamnati a yankunan Kosovo da ke da rinjayen yan Sabiya.

Admiral Stuart B. Munsch kwamandan kawancen sojojin ya ce matakin tura karin sojojin zuwa Kosovo muhimmin mataki ne da ya dace da kudirin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya.