Nau'ukan kyallayen rufe fuska a kasashen Afirka
Annobar COVID-19 ta sanya Afirkawa amfani da takunkumin fuska, sai dai dama amfani da kyallayen rufe fuskoki a musamman wasu yankuna na nahiyar, dadaddiyar al'ada ce.
Buzaye ne kadai masu amfani da kyallen rufe fuska a Libiya
Buzaye maza, su ne kadai ke amfani da nadi. Bisa al'ada, nadin nasu na ba su kariya ne daga barazanar fatalwa da ake kira "Kel Eru," da ke iya shiga jikinsu lokacin da suke tafiya a hamada. Tarihi ya nunar cewa ana rina rawuna da kyallayen Buzaye da sigini, wanda a wasu lokutan suke zama dabbare-dabbare a jikin masu shi. Saboda haka ne ma wasu ke kiransu,"masu launin shudi" na hamada.
Libiya: Rawani da kyallayen ba ce kariya kadai ga Buzaye ba
Hamadar Sahara da ta Sahel, yankuna ne da Buzaye ke kai komo a ciki tsawon lokaci a nahiyar Afirka. Da rawani da kuma kyallen rufe fuskar wadannan mutane na matsayin kariya gare su daga rairayin hamadar. Baya ga hakan sutura ce mai ba su kima da daraja. Wani abin kuma shi ne, sanya kyallen ga matashi tabbaci ne na balaga.
Libiya: Sutura ta cikin hamada
Buzaye dai mutane ne da ke cikin al'umar 'Berbers', da aka sani da rayuwar tafiye-tafiye a arewacin Afirka. A Nijar, suna kiran kansu "Imajeghen," a Aljeriya da Libiya kuma "Imuhagh," yayin da a Mali suke "Imushagh". Kalmar Tuareg da ake kiransu, ta samo asali daga harshen Berber da ya samo asali daga kalmar "Targa," wanda suna ne na wani lardi a Libiya.
Moroko: 'Yan kabilar Berber na sanya litham na al'ada
Ana kiran nadin al'ada na Buzaye a Moroko "Tagelmust" ko kuma "litham." Wannan hoton ya nuna yadda al'umar kasar ke amfanin da suturar a arewacin Afirka da ke yankin hamada. Mutumin da ake gani, dan kabilar Berber ne. Wadanda ke sanya irin wannan tufafin musamman lokutan rikici, kan sanya shi zama mai wuyar ganewa ko kuma saukin sajewa da al'ada.
Masar: Kabilun Bedouin ma na wannan shigar
Kamar Buzaye da 'yan kabilar Berber, su ma mutanen Bedouin, ba masu zama waje daya ba ne a rairayin hamada. Suna rayuwa a yankin kasashen Larabawan Afirka kamar Masar da kuma yankin Isra'ila. Ana kiran wannan dan rawani da wannan mutumin da ke hoton nan ke sanye da shi ''Kufiya'' a Masar; ko kuma "Ghutra" ko "Hatta" a wasu yankunan. Yanda ake nadin dai ya bambanta daga waje zuwa waje.
Mazan kabilyar Tubu na Chadi
Maza ne ba kuma mata ba ke amfani da kyalle wajen rufe fuskokinsu tsakanin 'yan kabilar Tubu da galibi ke zaune a yankin Tafkin Chadi. Mazan ne ke dinka kayayyakin. Sana'arsu dai ita ce kiwo, su mutanen Tubun. Sun kuma shahara ne a kiwon awaki da tumaki sai kuma wasunsu da ke da rakuma.
A Najeriya sarakuna na mafani da rawuna
Irin wadannan rawuna akan same su a Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda wannan da ya taba mulkin shiyar a yanzu ke sanye da shi. Muhammadu Sanusi II (lokacinnnadinsa a shekarar 2014). Aminu Ado Bayero ne ya gaje sarautar Kano a yanzu. Sarkin Kano, shi ne shugaba na biyu a tsarin shugabannin Musulunci bayan Sultan.
Mata kan yi amfani da Nikabi a Moroko
Mata Musulmi kan rufe fuskokinsu da nikabi. Rayuwa ce a yankunan Larabawa, sai dai ba su da yawa a yankin arewacin Afirka. Wannan matar na sanye ne da abaya ta al'ada da dankwali. Sai dai kasar Moroko ta haramta amfani da Burqa a shekara ta 2017. Ta yi hakan ne saboda wasu dalilai masu nasaba da tsaro.
Su ma a Somaliya, mata musulmi kan rufe jiki da hijabai da nikabi
Mata masu addini a Somaliya kan yi amfani da sutura dabam-dabam. A baya dai matan ba su rika sanya mayafan rufe fuska ba a kasar ta yankin gabashin Afirka. Sai dai sannu a hankali aka soma ganin karuwar mata masu amfani da hijabai tun misalin shekaru 1980 saboda karfin addinin Islama musamman a birane. Wadannan wasu dalibai ne a Mogadishu sanye da hijabi da niqab.
Mata ya yankin Zanzibar na Tanzaniya
A kudancin Zanzibar na Tanzaniya, mata na rufe fuskokinsu kamar wasu kasashen. Musulmi ne musamman daga cikin wadannan mata da ke amfani da wannan suturar a wannan tsibiri. Rufe fuskoki dai ba sabon abu ba ne a yanzu a baki dayan nahiyar Afirka.
A Kenya ana amfani da kyallayen zani wajen kare kai daga COVID-19
Sakamakon annobar Corona, amfani da takunkumi wajibi ne a cikin jama'a a Kenya. Ammam, ba kowa ke iya sayen wadanda ake jefarwa bayan aiki da su ba. A yankin Kibera da ke Nairobi, yankin da masu karamin karfi ke a ciki, David Ochieng na rarraba wadanda ake dinka su a kamfaninsa musamman saboda amfanin jama'a masu bukata.
Madinkin Kenya da ke samar da takunkumi ga kowa
Madinki Avido da ake gani a wannan hoto, na sanye da daya daga cikin takunkumin da ya dinka. Shi dai Avido ya taso ne a yankin Kibera. A wannan lokacin, ya kirkiro kamfaninsa na Lookslike Avido a birnin Kwalan na Jamus, wanda ya shahara da fito da abubuwa masu kare muhalli.
Dinkin takunkumin kare fuska a matsayin sana'a
Wata kafinta Sara Reeves, ta dakatar da aiki ala tilas a Nairobin Kenya sanadin annobar corona. Yanzu ita da sauran ma'aikatanta, sun koma aikin dinkin takunkumi. Suna amfani da atamfofi 'yan Afirka masu launuka kala-kala suna sayarwa. Sara Reeves ta ce; 'sayi daya ka sami guda kyauta' dabara ce ta samu da kuma kare jama'a daga cutar.
A Kenya kamar ko'ina, an ja damarar samar da takunkuman na fuska
Kimanin mata madinka 300 a wani kamfani a Nairobi, na dinka takunkumin dubu 20 a kullum. Wasu kamfanonin, sun ma sauya dabarar wajen dinka har ma kayan kariya na likitoci irin na asibitoci, galibin matan da a baya ba su da hikimar yin hakan. Hakan na faruwa har a kasashen irin su Mexiko da yankunan Falasdinu inda ake fama da karuwar bukatar wadannan kayayyaki.