1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nawaz Sharif ya koma Pakistan

November 25, 2007
https://p.dw.com/p/CSx4
Rahotanni daga Pakistan sun ce jirgin saman dake ɗauke da tsohon Firaministan ƙasar Nawaz Sharif ya sauka a birnin Lahore. Wani wakilin kamfanin dillancin labarun AFP ya ce ya ga lokacin da jirgin ya sauka. Gidan telebijin na kasar ya ba da sanarwar isar Sharif wanda shugaba Pervez Musharraf ya hambarad a wani juyin mulkin soji a shekarar 1999. A cikin watan satumba an hana Sharif shiga ƙasar lokacin da ya koma. Isar sa yau a Lahore ya kawo ƙarshen zaman gudun hijira na shekaru bakwai da Sharif ya yi a ketare. Sharif ya koma Pakistan ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa sakamakon dokar ta-baci da aka kafa a ƙasar.