1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Nazarin kutsen Ukraine a Rasha

Suleiman Babayo MA
August 22, 2024

Rasha tana nazarin kutsen da Ukraine ta kaddamar kan wani yanki na kasar inda dubban mutane suka tsere daga gidajensu.

https://p.dw.com/p/4jn8W
Yakin Ukraine
Yakin ynakin Kursk na Rasha bayan kutsen dakarun UkraineHoto: 95th Air Assault Brigade/via REUTERS

A wannan Alhamis Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasar domin tattauna yanayin da ake ciki a kusa da iyakar kasar da Ukraine, inda aka samu kutse na dakarun na Ukraine a yankin Kursk a farkon wannan wata na Agusta. Wannan kutse na dakarun Ukraine ke zama mafi girma da Rasha ta fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.

An dai yi fafatawa mai zafi tsakanin dakarun na Rasha da Ukraine, kafin daga bisa Ukraine ta karfafa ikonta a bayan wannan kutsen. Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya ce matakin kutse cikin Rasha wata dabara ce ta neman kawo karshen yakin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu kim,anin wtaanni 30 da suka gabata, bayan kutsen Rasha cikin wasu yankuna na Ukraine.

Wannan na zuwa lokacin da majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri'ar amincewa da shiga kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki. Haka ya zama muhimmin mataki na shiga kotun ta duniya. Akwai dai zarge-zarge da dama da Ukraine take yi wa Rasha kan aikata laifukan yaki tun bayan kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar.