Nazarin WHO: Motsa jiki yaro!
Ana kai yara makaranta bayan an ciyar da su da abincin kan hanya mai sa kiba. Yawancin matasa ba sa son motsa jiki a cewar wani sabon bincike na WHO. Wannan yana da mummunan sakamako ga al'umma baki daya.
Yara sun saba kai-kawo
Gudu, tsalle, hawa - kananan yara suna motsawa ko da yaushe. Suna bayyana yadda suke ji kuma suna aiwatar da abin da suka gani ana yi tare da taimaka wa juna. Ba sa son zama guri daya har sai sun kai wasu shekaru. Amma a cewar wani binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kwanan nan, fiye da kashi 80 na yara ‘yan shekara 11 zuwa 17 a duniya ba sa motsa jiiki.
Rashin motsi na haifar da damuwa
Kashi 85% na yaran mata da kashi 78% na yaran maza ba sa motsa jiki na tsawon awa guda a rana kamar yadda WHO ta ba da shawara. Wannan yana da sakamako maras kyau: Rashin motsa jiki yana haifar da rashin jin dadin rayuwa. Saboda motsi da wasanni sun kan haifar da farin ciki da annashuwa. Idan ana guje wa motsi, lalaci da damuwa da son fada za su karu.
Illar wasa a kan na'ura ga yara
Babu abin da ke hana yara motsa jikinsu kamar wasa a kan na'ura mai kwakwaluwa! Sautin da allon ke amayowa na jan hankalinsu. Sai dai neman raba su da wasan na jawo sabani da iyaye. Illolin wasan na da yawa: karfin hankalinsu na raguwa, sannan yana sa su kara nauyi sakamakon rashin motsa jiki.
Atisaye na rage ciwon jiki
Yawan motsa jiki na kara murdewar damtse. Kuma kyakkyawan damtse na haifar da kyakkyawan yanayin jiki. Amma rashin motsi yadda ya dace na sa ciwon baya da kuma ciwon kai. Sai dai irin wannan atisaye na da fa'ida saboda yakan sa kashin yara samun isasshen motsi: Karfin kashi na karuwa yayin da hadarin kamuwa da cutar kashi ke raguwa.
Kiyayi shan alawa!
Nura! Yaran da ke motsa jiki sosai za su iya samun damar saye ko shan alawa. Amma kayan zaki na zama hadari a duk lokacin da rashin motsa jiki ya kasa nika abincin da bai dace ba da ake ci. Haka kuma, sanin kowa ne cewa yara masu kiba kan sha wahala daga baya sakamakon kamuwa da cututtukan zuciya, irin su ciwon suga da hawan jini, zuwa bugun zuciya ko bugun jini.
Ana biyan rashin motsa jiki da tsada
Rashin motsa jiki da cin abinci mai yawa kuma maras inganci: Wadannan ne manyan matsaloli da yara da matasa da yawa ke fuskanta a kasar Chaina. A cikin wani lokaci na rayuwarsu, lafiyarsu na samun matsala. Komabaya da yake jawo wa al'umma baki daya na da yawa, kama daga farashin magani zuwa yin ritaya tun lokaci bai yi ba. Samun yara masu koshin lafiya zai zama ci gaba ga kowa da kowa.