Nema da ceton 'yan gudun hijira
Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta jima ta na bada agaji ga 'yan gudun hijira da ke kokarin shiga Turai ta tekun Bahar Rum. Wakilin DW Karlos Zurutuza ya shaida yadda aka ceto kimanin mutane dubu guda.
Shirin yin aikin ceto
Jiragen da suka hada da Phoenix da Argos da kuma "Dignity 1" ne kungiyar likitoci ta MSF ke amfani da su wajen ceton 'yan gudun hijira a Tekun Bahar Rum a wannan shekarar ta 2015. ''Dignity 1'' da ke da tsawon mita 50 ya ceci mutane kimanin dubu 5, yayin da sauran biyu suka ceto mutane dubu 11. Jiragen na aiki ne kusa da gabar tekun kasar Libiya.
Bacewa a cikin Teku
'Yan gudun hijira kan biya euro 500 don a ketara teku da su a cikin kananan jiragen ruwa na roba. Duk da hadarin da suke da su, sun fi irin jiragen da masu fasakwaurin mutane ke amfani da su. Jiragen robar ba su cika nutsewa ba kamar manyan jiragen wanda mafi yawanci kan kife da mutane kamar yadda wani matukin jirgin ruwa David Prados ya shaidawa DW.
"Mun kai ga ci!"
Galibin wadanda ke kan wannan jirgin ruwan wato "Dignity 1" sun shaidawa DW cewar masu fasakwaurin mutane a Libya sun ce wani babban jirgin ruwa zai cece su, kana ya kaisu Italiya. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin 'yan gudun hijira da bakin haure dubu 300 ne suka yi amfani da tekun Bahar Rum don shiga Turai.
Ceton mata da yara kafin maza
Yawanci a kan ceci mata da yara da ke kokarin ketara teku kafin a kai ga maza. Yara da mata kan kai kashi 10 ko 15 na wanda likitocin kungiyar MSF kan ceta daga jiragen ruwa kanana na 'yan gudun hijira. Galibin mata kan kasance da ciki wasu kuma da jarirai. Matan kan hau jirgin da ya cecesu ne a galabaice fiye da maza manya kuma su kan kasance cikin bukata ta duba lafiyarsu.
'Yan Afirka a kan jirgin ruwa
Ba kamar wadanda ke shiga kasashen yankin Balkan ba, galibin 'yan gudun hijirar da ake ceto a gabar ruwan Libiya 'yan kasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara ne. Libiya ta kasance wata babbar hanya da 'yan cirani da 'yan gudun hijira kan yi amfani da ita wajen shiga Turai duk kuwa da cin zarafi da ma kisan wasu da ake yi a kasar ta Libiya wadda ke arewacin Afirka.
Cinikin bayi
Wani dan gudun hijira daga Senegal wato Amin Jabi ya shaidawa DW cewa "Bayan da suka tsare ni a wata cibiya da ke Libiya, masu gadin wajen sun bani waya na kira dangi na don in shaida musu cewar za a kashe ni in ba su bada kudin fansa ba. Daga bisani sun sake ni. Galibi a kan sayar da wadanda suka kasa biyan kudin fansa a matsayin bayi don aiki a wuraren da ake gine-gine.''
Karshen fuskantar cin zarafi
Yawancin mata 'yan gudun hijira sun ce suna fuskantar cin zarafi daga maza da ke aiki a cibiyoyin da ake tsare bakin haure a Libiya. Baya ga duba lafiyar jiki da ta kwakwalwa, likitocin kungiyar MSF kan yi wa matan gwajin cutar nan mai karya garkuwar jiki wato AIDS ko SIDA bayan an cetosu. Galibin matan, inji wata jami'ar MSF, na cikin mawuyacin hali kuma labaran da suke badawa ba su da din ji.
Rashin yin bacci
Wata 'yar gudun hijira daga Najeriya Evelyn ta shaidawa DW cewa wasu maza biyar dauke da makamai sun kamata a wajen birnin Tripoli. Sun yi kokarin yi mata fyade amma kuma sai ya kasance ta na yin jinin al'ada, wannan ya sanya ransu ya baci har ma suka kai ga lakada mata duka batun da ya sanya ta fita hayyacinta. Mijinta daga bisani ya biya mata don ta tafi Italiya inda ta ce za ta je ta jira shi.
Hangen dala ba shi ne shiga birni ba
Kasancewar jirgin ruwa na ceton 'yan gudun hijira wato ''Dignity 1" bai da girma da sauri, ya kan kasance ne a gabar ruwan Libiya don yin musayar 'yan gudun hirar da za a kai Italiya a babban jirgin ruwa. Galibi mutanen kan sauka ne a tsibirin Sicily ko kuma tashar jiragen ruwa ta Reggio Calabria.
Tsammani marar tabbas
Galibin 'yan gudun hijira kan yi watsi da abinda zai faru bayan sun sauka daga jiragen ruwa. Za a kai wadannan mutanen ne arewacin Italiya inda za a kula da su na tsawon wata guda. Bayan nan da dama daga cikinsu za su fara kokarin in aiki don samun kudaden da za su aika gida sai da samun aikin fa na da wuyar gaske wanda hakan ka sanya wusu su shiga yin bara.