Neman diyya a Paris
October 31, 2023Talla
Masu karar dai na karar gwamnatin Gini don ta tilastawa ta basu diyya. Dama dai wata kotun ECOWAS ta umarci da a biya wadanda lamarin ya shafa diyyar kudi. Kusan shekaru 10 da suka gabata ne dai lamarin ya faru a wajen hakar ma'adinan kuza a kasar ta Gini inda mutane suka mutu yayinda wasu suka jikkata wasu kuwa aka tsare su bayan tarzumar da aka yi, kuma jami'an tsaron gwamnatin Gini sun yi amfani da karfi fiye da kima, don murgushe tarzumar kuma wadanda aka kama an azabtar da su, wanda kotun ECOWAS ta ce ya saba doka, kuma kotun ta nemi a biya su diyya ta kudi har dalar Amirka 536,000.