1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman hanyoyin yaki da Ebola

Zainab MohammedAugust 1, 2014

Shugabannin kasashen Gini da Saliyo da kuma Laberiya na can na yin taro a Conakry babban birnin kasar Gini domin lalubo bakin zaren shawo kan cutar Ebola da ke saurin kisa.

https://p.dw.com/p/1CngY
Hoto: picture-alliance/dpa

A yayin taron nasu dai za su kaddamar da shirin shawo kan cutar cikin gaggawa da zai lakume miliyan daya na kudin Euro. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce an ware wadannan kudaden ne domin samar da magunguna da kuma wadatattun ma'aikatan kiwon lafiya da za su yi aiki tukuru domin shawo kan cutar. Hukumar Lafiya ta Duniyar dai ta yi gargadin cewa cutar ta Ebola na neman gagarar kundila ganin yadda ta ke yaduwa tamkar wutar daji kuma cikin gaggawa. Shugabar hukumar Margaret Chan ce ta yi wannan gargadi yayin taro da shugabannin kasashen da suka fi fama da annobar Ebolan wato Laberiya da Gini da kuma Saliyo.

Mutane da dama sun hallaka sakamakon Ebola.

Kiyasin da Hukumar Lafiyar ta Duniya ta fitar dai na nunar da cewa kawo yanzu rayuka sama da 700 cutar Ebolan ta lakume ba ya ga wadanda ke kwance a asibitoci yayin da har yanzu ake ci gaba da samun rahoton bullar cutar. Tuni dai kasar Saliyo ta dauki matakin ko ta kwana inda ta bukaci sojoji da su yi kokarin killace wuraren da aka samu rahoton bullar cutar ta Ebola domin gujewa ci gaba da yaduwarta biyo bayan mutuwar daya daga cikin manyan kwararrun likitocin da ke yaki da cutar a Salo din Umar Khan. Kungiyar Likitoci na gari na kowa wato Doctors without boarders a Turance ta yi karin haske kan halin da ake ciki a kasar ta Salo. Dr. Sebastian Stein na daya daga cikin likitocin a Saliyo.

Wanke guraraen da masu Ebola suka kwanta da magunguna
Hoto: Reuters

Ya ce "In ka kalli mutane za ka tabbatar da cewa kowa a firgice ya ke idan ka kalli idanunsu za ka gane cewa lokaci kawai suke jira domin ba lalle ne su rayu ba". Ita kuwa Dr. Anja Wolz cewa take "A yanzu bamu da wani kuzari wajen yakar cutar abun ya fi karfinmu. Kamata ya yi mu dauki mataki kafin cutar ta Ebola ta iso gari amma yanzu kam mun makara matuka muna bukatar karin kwararru kan kiwon lafiya".

Mahukuntan Salo da Laberiya na daukar sabbin matakai

Ita ma dai shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana wasu jerin karin matakan kariya inda aka ba da hutu na tsahon wata guda.

Ta ce: "Daya ga watan Agusta ta zama ranar hutu kuma za a yi amfani da ita wajen wanke ma'aikatu da hukumomi da magungunan kashe kwayoyin cututtuka kuma dole ne kowa ya tafi hutu na tsahon kwanaki 30, ba bu wani banbanci za a rufe makarantu har sai an samu sanarwa daga ma'aikatar ilimi. Ma'aikatar lafiya da sauran hukumomi za su ci gaba da kokarin ganin an kone gawarwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar ta Ebola. Wannan matakin ya zama wajibi domin kare al'umma da ga kamuwa da cutur da kuma hanyoyin samar da ruwan sha".

Da dama dai na ganin cewa gwamnatin ta Laberiya da ta ke da wadanda suka mutu sakamakon cutar masu yawa ta yi sake wajen daukar matakan, mataimakin ministan kiwon lafiya kuma kakakin hukumar yaki da cutar Ebola na kasar ta Laberiya Tolbert Nyeswah ya yi karin haske.

Ebola Westafrika Liberia
Hoto: Reuters

Yace: "Na yarda da ku cewa ya kamata ace mun dauki matakan da wuri, sai dai koda al'ummomin kasa da kasa suma sun makara kasancewar kasashe uku suna ta faman kokawa da musibar da ta afka musu ta annobar Ebolan amma sai yanzu Hukumar Lafiya ta Duniya ke yin taro a Conakry bayan cutar ta hallaka sama da mutane 700. A yanzu maganar da nake mutane da dama na kara mutuwa kuma wasu suna kara kamuwa da cutar".

Sai dai a nasa bangaren shugaban hukumar yaki da cutar ta Ebola na kasar Gini Conakry ya soki wannan mataki da kasashen biyu suka dauka inda a ganinsa kyale musamman yara 'yan makaranta kara zube sakamakon rashin zuwa makaranta ba tare da an killacesu ba ka iya kara ta'azzara yaduwar cutar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu