Neman haɗin kan Iran game da rikicin Siriya
August 29, 2012Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya gana da jagorar addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei da kuma shugaba Mahmoud Ahmadinejad a wannan Larabar, inda kuma zai halarci taron ƙungiyar ƙasashe 'yan ba ruwanmu da ƙasar ta Iran ke karɓar baƙuncin sa.
Gabannin ganawar dai kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Ban Ki Moon ya na bayyana fatan cewar jagorancin ƙungiyar da Iran za ta yi cikin shekaru ukku masu zuwa za su taimaka wajen shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta. Daya taɓo batun Siriya kuwa Ban Ki Moon ya ce akwai muhimmiyar rawar da Iran za ta taka wajen warware rikicin da ƙasar ke fuskanta, inda ya ce tattaunawar da zai yi tare da jami'an ƙasar ta Iran za ta mayar da hankali ne akan rikicin.
Ziyarar farkon da Ban Ki Moon ya taɓa kaiwa Iran dai ta kasance ne a shekarun 1970 sa'ilin daya ke matsayin ministan kula da harkokin wajen Koriya Ta Kudu. Hakanan a lokacin wannan ziyarar ana sa ran zai ci abincin rana tare da shugaban majalisar dokokin Iran Ali Larijani.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou